Jigo a jam’iyyar APCn kano kuma babban mai taimaka wa Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Faizu Alfindiki, ya musanta ikirarin da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi na cewa yana daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC.
Faizu Alfindiki ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24 a ranar Asabar. Ya bayyana cewa babu wata shaida a tarihi da ke nuna cewa Kwankwaso ya na cikin wadanda suka taka rawar gani wajen kafa jam’iyyar, domin kuwa ba ya cikin jam’iyyun da suka hadu wajen samar da APC a shekarar 2013.
Ya ce jam’iyyun da suka dunkule suka kafa APC sun hada da CPC karkashin marigayi Janar Muhammadu Buhari, da ACN karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, APGA karkashin Sanata Rochas Okorocha, da kuma ANPP karkashin Kashim Shettima, marigayi Bukar Abba Ibrahim, Malam Ibrahim Shekarau da Yariman Bakura.
Rundunar yansanda ta Kano ta kama wasu da suna yi fashi da makami a Lagos
Alfindiki ya kuma bayyana cewa wasu fitattun ‘yan siyasa kamar Rotimi Amaechi, Aliyu Wamakko, Murtala Nyako da Bukola Saraki ne suka shiga jam’iyyar daga baya a 2014, shekara guda bayan kafa ta.

Duk da haka, ya amince da cewa shigar Kwankwaso cikin jam’iyyar ya taimaka mata a zaben 2015, inda ya samu kujerar Sanata, mataimakinsa ya zama gwamna, sannan APC ta lashe dukkanin kujerun yan majalisar tarayya dana jihar Kano.
Alfindiki ya ce kamata ya yi Kwankwaso Sai ya ci gaba da godewa jam’iyyar APC domin ita ce ta farfado da siyasar sa a lokacin da ta ke dab da rushewa.