Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta bayyana samun gagarumar nasara a binciken da ta gudanar kan wani mummunan harin fashi da makami da kuma yunƙurin kisa da ya faru a Bera Estate, Chevron, Legas.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikowa Kadaura24, dakaru Rundunar na musamman ne suka cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin a ranar 11 ga Satumba, 2025 a unguwar Na’ibawa, Kano.
Wadanda aka kama sun haɗa da:
Mathew Adewole, mai shekaru 25 daga Na’ibawa Quarters, Kano.
Mukhtar Muhammad, mai shekaru 31 daga Unguwa Uku Quarters, Kano.
Mathew Adewole ya amsa cewa shi ne ya kai hari kan wani mazaunin Bera Estate mai suna Lil-Kesh a ranar 19 ga Agusta, 2025. Ya yi masa mummunan rauni a wuya, a kokarinsa na yin fashi da kuma kisa.
Ya tilasta wa wanda aka kai wa harin ya tura naira miliyan 2 da dubu 120 (₦2,120,000) daga asusunsa ta wayar salula zuwa asusun Mukhtar Muhammad.
A cewar sanarwar, rundunar ta bi umarnin babban sifetan ‘yan sanda na kasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, wajen ƙara ƙarfin masu leken asirinta da kuma haɗa gwiwa jama’a domin dakile miyagun laifuka.

An mika waɗanda ake zargin ga rundunar ‘yan sanda ta Jihar Legas domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori ya yaba da ƙoƙarin jami’ansa da kuma haɗin kan jama’a, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da aiki tukuru wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.