Gwamnatin Kano ta rufe wasu makarantun masu zaman kansu

Date:

 

Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu da na sa kai ta Jihar Kano (KSPVIB) ta dauki matakin rufe wasu makarantu guda takwas da ke aiki a fadin jihar, bisa dalilai na karya dokoki da kuma sabawa ƙa’idojin gudanarwar hukumar.

A yayinda yake ganawa da manema labarai, Shugaban hukumar Kwamared Baba Umar ya ce rufe makarantun ya zama wajibi saboda karya dokokin kara kuɗin makaranta da rashin yin takardun na izinin gudanarwa.

Wadannan makarantu sun hada da:

1. Prime College Kano – Alu Avenue, Kano

2. Darul Ulum – Hotoro (Ahmad Musa Road)

3. Gwani Dan Zarga College – (Kofar Waika)

Gwamna Abba ya zargi Ganduje da wawure kudaden Kano ba tare da tabuka komai ba

4. Awwal Academy – Rimi (Sumaila)

5. Dano Memorial College – (Sumaila)

6. Unity Academy – Wudil

7. Nurul Islam School

8. As-Saif College.

FB IMG 1753738820016
Talla

A makon da ya gabata ne shugaban hukumar Baba Umar ya bada wa’adin mako biyu a kai korafin duk wata makaranta mai zaman kanta da ta kara kuɗin makaranta,Inda yace mutane sun bada hadin mai kuma su sun dauki matakin da ya dace na rufe irin wadannan makarantu tare da gurfanar da su gaban kotu.

Shugaban yace a bisa umarnin Kotu,an dakatar da ayyuka a wadannan makarantun har sai abinda alkali ya yanke hukunci akai.

Yace wasu sun ƙara kuɗin makaranta ba tare da amincewar gwamnati ba.

Baba Umar ya kuma ce sun gano matsalar tsaro da rashin isasshen tsari a cikin gine-ginen wasu daga cikin makarantun.

Sai kuma rashin ingantattun kayan aiki da guraben koyarwa da ya dace da ƙa’idar karatun zamani.

Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki ya zama dole ne domin tabbatar da cewa yara na samun ilimi mai inganci, tare da kare iyaye daga karɓar nauyin kuɗaɗen da aka ɗora musu ba bisa ƙa’ida ba.

Ta kuma yi gargadi ga sauran makarantu masu zaman kansu a jihar da su kiyaye doka da ƙa’idojin gwamnati, inda ta ce duk wanda ya ci gaba da karya dokoki, ba za a yi masa rangwame ba.

Daga karshe ya nemi jama’a su cigaba da kai Rahoton duk makarantar da ta saba doka yana mai cewa ba’a kafa hukumar sa domin kuntatawa makarantun masu zaman kansu ba saidai domin dawo da su kan hanya idan sun kauce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar ODPMNigeria ta shirya taron tattaunawa da matasa a Bichi

Daga Ahmad Isa Getso   Ƙungiyar Rajin Kawo Sauyi da Cigaba...

Yadda Dansanda ya harbe kansa da bindiga a Kano

Wani jami’in dansanda mai suna Aminu Ibrahim ya rasa...

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin aikin hajjin badi

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince...

Kudade: Ganduje ya caccaki Gwamnatin kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon shugaban jam’iyyar APC...