Inna lillahi wa’inna ilaihirrajun
Allah ya yiwa Sarkin Gabas kuma Hakimin Kabo Alhaji Idris Adamu Dankabo Rasuwa.
Alhaji Idris Adamu Dankabo ya rasu, ya na da shekaru 48.
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayi Alhaji Idris ɗa ga marigayi Jarman Kano, Alhaji Muhammad Adamu Dankabo, ya rasu ne sakamakon haɗarin mota da yayi a cikin Birnin Kano.
Ya rasu ya bar mata ɗaya da ƴaƴa biyu.
Nasarar da Ɗaliban Kano suka Samu a NECO Kokari ne na Gwamnatin Ganduje – Sanusi Kiru
Za a yi jana’izar sa a yau Juma’a da misalin ƙarfe 10 na safe a fadar Sarkin Kano, Kofar Kudu, inda ake sa ran Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ne zai yi masa sallah.
Allah Ya gafarta masa, Ya sa aljanna ce makomar sa.