Zargin ta da hargitsi: Tsagin Ganduje sun yi Karar Tsagin Shekarau wajen IG

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Bangaren Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje sun zargi tsagin Sanata Malam Ibrahim Shekarau da kokarin tada tarzoma a jihar kano ,ta hanyar sayan Makamai da Kuma tunzura Matasa.
Hakan na kunshe ne cikin takardar korafin da Suka rubutawa Babban Sufeton Yan Sanda na Kasa wadda Sanata Kabiru Gaya da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar wakilai Hon. Alhassan Ado Doguwa da wasu yan Majalisun jiha dana Tarayya guda da Shugabanin Kananan Hukumomi suka Sanyawa Hannu.
A Cikin takardar sun bukaci Babban Sufeton Yan Sandan da ya Gudanar da bicike tare da daukar Matakin gaggawa akansu don Samar da Zaman Lafiya a Jihar Kano.
Cikin takardar korafin da Kadaura24 ta samu ta nuna yadda aka yi sitamfi na Ofishin Babban Sufeton Wanda hakan ke nuna Ofishin ya karbi takardar korafin ta su.
Idan ba’a mantaba Kadaura24 ta rawaito a kwanakin bayan tsagin Sanata Malam Ibrahim Shekarau Suma sun rubuta makamancin irin Wannan takarda ta korafi ,Inda Suka zargi tsagin Gwamna Ganduje da Kona ofishin Sanata Barau Jibril a Ranar 30 ga Watan Nuwanba 2021.

1 COMMENT

  1. קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. מכוני ליווי

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...