Saminu Ibrahim Magashi
A yauma kotun Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ta fara zamanta ne da misalin karfe 9 na safe inda Kuma aka fara da gabatar da lauyoyin dake gabatar da Kara.
A Zaman wannna rana lauyoyin dake kare Wanda ake kara Suka gabatar da sabuwa fuska a matsatsayin Wanda zai jagoranci tawagar lauyoyin da zasu cigaba da kare Abduljabbar kabara mai suna A.O Muhammad Mai lamabar kwarewa ta SAN.
Bayan gabatar da Lauyoyin kotu ta umarci a gabatar da sheda na uku Wanda ya fara da gabatar da sunansa da cewa sunansa Inspector Mohd Kabiru ma’aikaci a sashen binciken manyan lefuka dake helkwatar yan sanda ta jihar kano bomfai, lnda yafara da cewa a ranar 6/7/2021 Sun sami rubutaccen umarni daga kwamishinan yan sanda na jihar kano cewa suyi bincike kan korafi da aka kawo gabansu akan Abduljabbar kabara Inda aka ce ana zarginsa da batanci ga fiyayyiyen halitta tare da kuma yunkurin tada tarzoma a jihar kano, Kuma sunyi amfani da kwarewarsu inda suka je kafa da kafa har gidan malamin dake filin mushe tare bayyana zargin da ake yi akansa , Sai dai malamin ya musanta inda yace a kokarinsa na kare fiyayyiyen halittane wasu da basa sason zaman lafiya ne suka yanke Masa Karatun don Kawai su hallakashi Kuma ya basu arubuce. Kazalika Shaidan yace bayan sun gayyaci malamin offishinsu bai amsa gayyatar ba .
Anasa bangaren Abduljabbar ya yin da aka bashi damar suka tare da tambayoyi ga shaidan ya bayyana cewa tun kafin su je gidansa suka gayyace shi Kuma ya amsa wannan gayyatar ba kamar yadda shaidan ya fadawa Kotu ba.
Bayan da aka gama da tambayoyi kotu ta sallami shaidan Sannan ta bayyana cewa ta boye ra’ayinta akan amsar shaidar ko kuma kin amsarta.
Bayan hakan ne lauyan gwamnati ya roki kotun da ta kara musu damar karo wasu shaidun a zama nagaba.
Shima lauyan Wanda ake kara ya roki kotu da ta basu musu belin Wanda yake karewa, Amma dai kotun taki aminta rokon bada belin.
Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya sake dage sauraren shari’ar har zuwa ranar 23/12/2021 domin dawowa adora daga inda aka tsaya.