Da dumi-dumi: Mafarauta sun kama masu garkuwa da mutane a jejin Jihar Kogi

Date:

 

Mafarauta sun samu nasarar cafke wasu da a ke zargin masu garkuwa da mutane ne guda uku a maɓoyar su, kusa da yankin Ossra-Irekpeni a kan hanyar Okene-Lokoja-Abuja.

Ɗaya da ga cikin mafarautan da su ka kai sumamen ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa sai da a kai musayen wuta kafin su damƙe mutanen.

Ya ce mafarautan, tare da shugaban Ƙaramar Hukumar Adavi, Joseph Samuel Omuya, su ka kutsa kai cikin dajin bayan samun bayanan sirri.

Daily Nigerian ta rawaito Mafaraucin yana baiyana cewa , bayan sun shiga jejin, sai masu garkuwa da mutanen su ka fara buɗe wuta, sai mafarautan su ka maida martani.

“Nan da nan muna muka buɗe musu wuta har mu ka samu nasarar damƙe uku daga ciki,” in ji shi.

Ya kuma ƙara da cewa wasu daga cikin ƴan ta’addan sun tsere da raunukan bindiga a jikin su.

Bayan Omuya ya yabawa mafarautan a bisa ƙoƙarin da su ka yi na kama ƴan ta’addan, ya kuma yi kira ga mazauna ƙauyuka da su zama su na jajircewa wajen tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...