Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tafi kasar Amurka inda yake halartar wani shiri na tsawon mako Guda akan jagoranci.
KADAURA24 ta rawaito Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa Gwamna Ganduje na halartar wani shiri na inganta jagoranci na kwarai a makarantar kasuwanci ta Harvard da ke Boston.
Ya ce gwamnan ya mika mulki kuma ya ba mataimakin gwamna Dakta Nasir Yusuf Gawuna cikakkiyar damar zama mukaddashin gwamnan jihar.
Sanarwar ta kara da cewa duk wata harkokin mulki daga yanzu sai an bi ta ofishin mataimakin gwamna domin daukar matakin da ya dace.