Daga Cikin Albashin Sa, Shugaban Kano Poly ya sake Rabon Naira Dubu Biyar-Biyar a Dawakin Tofa

Date:

Daga Musa Mudi Dawakin Tofa.
5, ga Disamba 2021
Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano Dr. Kabir Bello Dungurawa ya shiga mazabar Dawaki Gabas a karamar hukumar Dawakin tofa don bada tallafin naira dubu biyar- biyar ga iyayen marayu da sauran mabukata guda ashirin a ranar Lahadi 5 ga watan Disamba, 2021.
Dr Dungurawa ya ce ” a duk karshen wata yana cire naira dubu dari daga cikin albashinsa don tallafawa masu tsananin bukata ashirin-ashirin daga kowacce mazaba dake  karamar hukumarsa ta Dawakin Tofa.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban na Kano Poly ya kara da cewa yana bada tallafin ne ga al’ummarsa saboda daga cikinsu ne Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya zaboshi ya kuma bashi matsayi na Rector don ya shugabantar Kwalejin”.
Mazabar Dawaki Gabas ita ce mazaba ta biyar cikin mazabu goma sha daya da suka amfana da tallafin a wannan rana ta Lahadi” Inji Dr. Dungurawa.
A yayin taron bada tallafin mataimakin sakataren kungiyar malaman makarantun gaba da sakandire ‘yan Karamar hukumar Dawakin Tofa kuma malami a kwalejin Ilimi ta tarayya dake Bichi Malam Mustapha Hassan Hashim ya ce kungiyarsu aka dorawa alhakin zabowa da tantance duk wadanda suka amfana da tallafi na Dr Dungurawa.
  Yace suna zabo Mutane ne daga cikin dimbin mata  iyayen marayu mabukuta da kuma mazan dake cikin halin matsin rayuwa ashirin daga mazabar Dawaki Gabas domin tallafa musu da naira dubu biyar-biyar ya kuma yi kira ga sauran masu hali da dama cewa su yi koyi da Dr Dungurawa.
Kansilan Mazabar Dawaki Gabas Hon. Abdussalam Ishaq ‘Yarkanya ya godewa Allah sannan ya yabawa Dr Kabir Bello Dungurawa da ya zo mazabarsa domin  tallafawa alummarsa.
Shugaban Kwalejin Dr. Dungurawa ya bada tabbacin zai cigaban da tallafawa al’ummar sa domin rage musu radadin halin matsin rayuwa da ake ciki a wannna Lokaci.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...