Ku san kan ku kafin ku yi komai a rayuwarku – Turakin Kano ga al’umma

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Turakin Kano Hakimin Gwale Alhaji Mahmoud Ado Bayero ya bukaci al’umma da su fara sanin kan su kafin su yi kokarin sanin wani abu a dgd wanda ta haka ne za su sami cigaban da ya dace.

Alhaji Mahmud Ado Bayero ya bayyana hakan ne wajan taron ga fili ga mai doki, wanda sashin Hausa na kwalejin ilmi ta Aminu Kano AKCOE hadin guiwa da jami’ar tarayya ta FUDMA, da kuma kungiyar daliban Hausa karkashin jagorancin kwamared Abubakar Sabo su ka shirya.

InShot 20250309 102512486
Talla

Ya ce ta hanyar sanin kai ne za ka san kana da kima da daraja don haka ya bukaci kowanne Bahaushe da ya dinga dabbaka dabi’un sa a duk in da ya sami kan shi, domin nuna cewa ya san kan sa.

A nasa jawabin shugaban makarantar Dakta Ayuba Ahmad Muhammad cewa ya yi sashin Hausa sun san abun da su ke yi wajan gabatar da ayyukan su don haka za su cigaba da ba su hadin kai da duk wata gudunmawa duk sanda za su gabatar da wani abu, da shafe su.

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya nada sabbin masu ba shi shawara

Anasa bangaren farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, bayyana cewa an shirya taron ne don a fadi ka’idoji da sharudda da ya kamata a yi waka ta furuci a kuma yi kida a sadar da shi ga al’umma.

Shi kuwa makadin da ya gafarta da kidan shi a wajan Alhaji babangida kakadawa cewa ya yi, dama can yanayin wakokin na sa ne don ilmantarwa da fadakarwa da kuma wa’azantarwa.

Dr Mahe Isah Ahmad shi ne shugaban sashin, na Hausa a makanatar ya ce taron na iya na dalibai ba ne, na duk wani mai kishin Hausa ne, kuma shi ne karo na farko a tarihin kafuwar makarantar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...