Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar wakilai ta Kasa Kuma Dan Majalisar dake wakiltar Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada Hon. Alhassan Ado Doguwa ya Mika Sakon ta’aziyya da jajantawa ga al’ummar Jihar Kano bisa Iftila’in hatsarin jirgin Ruwa (kwale-kwale) a Garin Bagwai.
Sakon ta’aziyyar na kunshe ne Cikin Wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Shugaban Majalisar wakilai Auwal Ali Sufi ya sanyawa hannu Kuma aka aikowa Kadaura24.
Sanarwar ta ce Shugaban Masu Rinjaye Wanda shi ne Sardaunan Rano ya kadu sosai Lokacin da ya Sami labarin hadarin Wanda yayi sanadiyyar Rasuwar Ɗalibai kusan 27 da Kuma Waɗanda Suka jikkata.
Tallafi :Alhassan Ado ya raba Naira Miliyan 70 ga al’ummar Tudun Wada da Doguwa
” Wannan Lamari al’amari ne daga Allah Wanda Babu wanda ya Isa ya Hana faruwar sa, Amma dai lamarin bai yi mana dadi ba, muna addu’ar Allah ya gafartawa Waɗanda Suka rasu, Waɗanda Suka jikkata Kuma Muna fatan Allah ya basu Lafiya”. Inji Hon. Doguwa
Hon. Doguwa ya Mika Sakon ta’aziyya da jajantawa ga Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da al’ummar Karamar Hukumar Bagwai dama na Jihar kano baki daya.
Hon. Alhassan Ado Doguwa ya yi fatan Allah ya baiyana Waɗanda Suka nutse a Cikin Ruwan, Sannan yayi fatan Allah ya Kare afwar hakan anan gab.