Tinubu zai mayar da Fubara kan kujera gwamnan Rivers amma ya gindaya masa sharadi- Rahoto

Date:

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar da Siminalayi Fubara a matsayin Gwamnan Jihar Rivers — amma da sharadin cewa ba zai sake tsayawa takarar shugabancin jihar a 2027 ba, kamar yadda rahoton TheCable ya bayyana.

An cimma wannan yarjejeniya ne a wani taro da aka gudanar a daren Alhamis a fadar shugaban ƙasa, inda Tinubu ya karɓi bakuncin Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT); Gwamna Fubara; Martin Amaewhule, shugaban majalisar dokokin jihar da aka dakatar; da wasu ‘yan majalisa.

InShot 20250309 102512486
Talla

Majiyoyin fadar shugaban ƙasa sun bayyana wa TheCable cewa wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi don dawo da tsarin dimokuraɗiyya a Jihar Rivers, kuma yana kunshe da gagarumin yarjejeniya da sauye-sauye.

Bisa bayanan da suka fito daga cikin masu ruwa da tsaki, ɗaya daga cikin muhimman sharuɗɗa shi ne a ba Fubara damar kammala wa’adinsa na shekaru huɗu, amma ya hakura da kowanne yunƙuri na neman wa’adi na biyu a 2027 — wani mataki da zai rage masa ƙarfi a siyasa, amma ya amince da shi.

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Wata majiya ta bayyana cewa a cikin yarjejeniyar, Wike zai sami damar zaɓar dukkan shugabannin ƙananan hukumomi guda 23 na jihar.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Majiyar daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa hakan zai ba Wike babbar dama a siyasa, musamman wajen riƙe ikon siyasa daga tushe a matsayin Ministan Abuja.

TheCable ta kuma gano cewa Fubara ya amince da biyan dukkan hakkokin da ake bi na ʼyan majalisar jihar guda 27 da suka goyi bayan Wike waɗanda aka dakatar.

A sakamakon haka, ‘yan majalisar ba za su ƙaddamar da yunƙurin tsige Fubara daga mukaminsa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...