Kotun majistiri dake zamanta a Noman sland karkashin Mai sharia Hadiza Mahammad Hassan ta aike da Umar Hisham fagge wanda ake kira tsulange zuwa Gidan Gyaran hali da tarbiya.
Tun da fari dai Hukumar tace Fina Finai ta jihar kano ta kamashi tare kuma da gurfanar da shi gaban kotun.

Wakilin Kadaura24 da ya halarci zaman Kotun ya ce tuni an tusa kyeyar Matashin zuwa gidan gyaran hali har zuwa ranar 3 ga watan yuli , 2025.
Kotu ta yanke wa Jarumin Kannywood, Kilina hukuncin shekara 1 a gidan yari
Dama dai al’ummar jihar Kano sun jima suna kokawa da yadda Matashin ke gudanar da harkokinsa na Wasan barkwanci, inda yake amfani da rigar mama ta mata tare kuma da tare hanya duk da sunan Wasan barkwanci.
Karin bayani zai zo daga baya…