Yadda akai Hargitsi ya barke a taron APC na Arewa maso yamma

Date:

An samu saɓani a wani taron shugabannin jam’iyyar APC a yankin Arewa Maso Gabas da aka gudanar a Jihar Gombe.

Rikicin ya fara ne bayan da Kwamared Mustapha Salihu, Mataimakin Shugaban APC na ƙasa mai kula da Arewa Maso Gabas, ya bayyana goyon bayansa ga takarar Shugaba Bola Tinubu don ya sake tsayawa takara a karo na biyu.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Sai dai bai ambaci sunan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ba.

Manyan jiga-jigan jam’iyyar APC daga yankin sun halarci taron, ciki har da gwamnoni, ministoci, da ‘yan majalisa.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, shi ma ya halarci taron.
Bayan Salihu ya gama jawabi, wasu daga cikin mahalarta taron sun fusata.

Farfesa Gwarzo Ya Samu Lambar Karramawa A Faransa, Wakiliyar UNESCO Ta Halarta

 

Take suka fara yi masa ihu, wasu ma suna barazanar kai masa hari.

Sai jami’an tsaro sun fito da shi daga ɗakin taron don kare lafiyarsa.

Don kwantar da rikicin da ya taso, Mataimakin Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Bukar Dalori, ya fito ya bayyana goyon baya ga Tinubu da kuma Shettima don su ci gaba da mulki.

Amma lamarin ya ƙara dagulewa bayan da ya yi jawabi, inda ya ayyana goyon bayansa ga Tinubu kaɗai, ba tare da ya ambatar sunan Kashim Shettima ba.

A yayin jawabin da ya yi na kusan minti 10, Ganduje bai ambaci sunan Shettima ba.

Shi ma sai da jami’an tsaro suka fita da shi daga wajen taron saboda gudun rikicin da zai je ya dawo.

Shettima dai ɗan Jihar Borno ne, ɗaya daga cikin jihohin yankin Arewa Maso Gabas.

InShot 20250309 102403344
Mutane da dama sun ji ba ɗadi kan rashin ambaton sunan Kashim Shattima a wajen taro da aka yi a yankinsa.

Taron ya kare cikin gaggawa saboda tashin hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...