Farfesa Gwarzo Ya Samu Lambar Karramawa A Faransa, Wakiliyar UNESCO Ta Halarta

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Jami’ar Cité Universitaire de Paris, daya daga cikin fitattun jami’o’i a Faransa da ake darajawa, wacce ke matsayi na 12 a fadin Turai, ta karrama Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, Shugaban Ƙungiyar Jami’o’i Masu Zaman Kansu na Afirka (AAPU), da Lambar Girmamawa mai daraja saboda gudunmawar sa wajen bunkasa ilimi a Afirka da ma duniya baki ɗaya.

An mika lambar yabon ne a ranar Juma’a, 13 ga watan Yuni, 2025, ta hannun Shugaban Jami’ar, Sanata Jean Mac Sauve, inda aka gudanar da bikin a matsayin wani bangare na shagulgulan cika shekaru 100 da kafuwar jami’ar, da kuma wani taron kasa da kasa kan bunkasa ilimi da bincike a Afirka.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Taron ya samu halartar manyan masana daga jami’o’i daban-daban na duniya. A jawabinsa, Sanata Jean Mac Sauve ya bayyana jin daɗinsa da irin rawar da Farfesa Gwarzo ke takawa wajen wakiltar Faransa cikin kima a Afirka, kasancewar sa ɗan tsohuwar makarantar ta Faransa.

Ya yabawa Farfesa Gwarzo kan yadda yake zuba hannun jari a bangaren ilimi tare da sadaukarwar da yake yi wajen bunkasa manyan makarantu a Nijeriya da Afirka baki daya, yana mai cewa hakan abin yabo ne matuƙa.

Wakiliyar Dindindin ta Nijeriya a UNESCO, Jakadiya Dr. Hajo Sani, ita ce ta wakilci Nijeriya a wajen bikin, inda ta yabawa jami’ar bisa zaɓar Farfesa Gwarzo a matsayin wanda ya cancanci wannan girmamawa. Ta ce wannan yabo babbar shaida ce kan jajircewar Farfesan wajen ci gaban ilimi da tasirinsa ga al’ummar ilimi gaba ɗaya.

Kwacen waya: Ya kamata gwamnatin Kano da hukumomin tsaro su tashi tsaye – Auwal Danlarabawa

Jakadiya Hajo Sani ta kara da cewa Farfesa Gwarzo ya ba da gudunmawa sosan gaske kuma mai tsoka ta hanyar kafa jami’o’i guda uku a Nijeriya, inda ta bayyana cewa har ‘ya’yanta biyu suna daga cikin waɗanda ke cin moriyar wannan gagarumin ci gaba.

A nasa bangaren, Farfesa Gwarzo ya nuna godiya ga jami’ar ta Faransa bisa wannan lambar girmamawa da aka ba shi, yana mai nanata kudurinsa na ci gaba da inganta harkar ilimi ba kawai a Afirka ba, har ma a duniya baki ɗaya.

Ya kuma yi kira ga dukkan ‘yan Afirka da ke karatu a ƙasashen waje da su dawo gida bayan kammala karatu, domin ba da gudunmawa wajen gina nahiyar Afirka da har yanzu ke da buƙatar ci gaba.

InShot 20250309 102403344

A karshe, Farfesa Gwarzo ya ce wannan lambar yabo za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da jagorantar gamayyar jami’o’in MAAUN zuwa ga samar da ingantaccen ilimi mai tasiri ga ci gaban rayuwar al’umma.

Lambar Girmamawar ta zama wata kwakkwarar shaida ta irin tasiri da sadaukarwar Farfesa Gwarzo wajen haɓaka ilimi a matakin duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...