Hukuncin Kotu ya Shafi Zaben Shugabanin Mazabu ne Kawai – Muhd Garba

Date:

Daga Zainab Muhd Darmanawa
 Jam’iyyar APC a jihar Kano ta ce hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar Talatar da ta gabata ya shafi zabukan Shugabanin jam’iyyar APC na matakan mazabu ne kawai ba shugabannin jam’iyyar na jiha ko na kananan hukumomi ba.
 A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya ce Shugabannin jam’iyyar a jihar har yanzu su hedikwatar jam’iyyar ta amince da su a Matsayin halasttun Shugabanin.
 Sai dai ya ce jam’iyyar zata saukaka  kara ne don kalubalantar hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.
 Malam Garba ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su kwantar da hankulansu su ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.

19 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rashin tsaro: Tinubu na ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro na ƙasa

A halin yanzu shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na...

Ban ce filin makarantar Bechi nawa ba ne, Kuma zan taimaka wajen gini Makarantar – Alh. Sagir Jaen

Daga Maryam Muhammad Ibrahim Biyo bayan koken da al'ummar garin...

Ƴan majalisar wakilai 2 na NNPP a Kano sun fice daga jam’iyyar zuwa APC

Wasu ‘yan majalisar wakilai biyu daga jihar Kano sun...