Hukuncin Kotu ya Shafi Zaben Shugabanin Mazabu ne Kawai – Muhd Garba

Date:

Daga Zainab Muhd Darmanawa
 Jam’iyyar APC a jihar Kano ta ce hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar Talatar da ta gabata ya shafi zabukan Shugabanin jam’iyyar APC na matakan mazabu ne kawai ba shugabannin jam’iyyar na jiha ko na kananan hukumomi ba.
 A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya ce Shugabannin jam’iyyar a jihar har yanzu su hedikwatar jam’iyyar ta amince da su a Matsayin halasttun Shugabanin.
 Sai dai ya ce jam’iyyar zata saukaka  kara ne don kalubalantar hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.
 Malam Garba ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su kwantar da hankulansu su ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.

19 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...