Hatsarin Jirgin Bagwai Iftila’i ne ga Kano Baki daya – In ji Gwamna Ganduje

Date:

Daga Maryam Abubakar Nice
 Hatsarin kwale-kwalen daya faru a Bagwai, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20, yayin da ake ci gaba da aikin ceto Wasu da hatsarin ya rutsa dasu Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana hatsarin a matsayin Iftila’in daya shafi duk al’ummar Jihar Kano.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne Cikin Wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran as Malam Abba Anwar ya Sanyawa Hannu Kuma ya aikowa Kadaura24.
 “Mun samu labarin cewa jirgin ya taso ne daga Hayin Badau zuwa Bagwai a kan hanyarsu ta zuwa halartar bikin Mauludi, yayin da jirgin ke dauke da mutane kusan 50 dauke da wasu kaya, wanda ya kife saboda da yawa Nauyin da aka yi Masa, Kuma yawancin Mutanen ciki daliban Islamiyya ne.” A cewar  gwamnan.
 “A yayin da muke addu’ar Allah ya gafartawa wadanda suka rasu ya kuma baiwa wadanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa, ina kira ga matuka irin Wadancan jiragen ruwa da su dai daukar Mutanen da suka wuce kima don gudun salwantar da rayukan al’umma.
 Ya kamata su sani cewa har yanzu za su iya samun riba ba tare da yin lodin da ya wuce kima ba a Cikin kwale-kwalensu ba,” in ji Ganduje.
 “Ya zuwa yanzu, bisa ga bayanin da muka samu, domin a safiyar yau Laraba an samu mutuwar mutane 20, yayin da Mutane 7 ke kwance a asibiti, an kuma gano wasu 8 a safiyar yau kuma ana ci gaba da aikin ceton wasu, muna jinjina wa jajircewa da kishin kasa.  na kungiyoyin bada agaji” in ji shi.
Idan ba’a mantaba taba Shekaru sama da goma da suka gabata an taba Samun irin Wannan hatsarin kwale-kwalen Wanda shi ma ya yi sanadiyyar mutuwar Mutane da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...