Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talatar nan, ta umurci gwamnatin jihar Kano da ta Nemi afuwar tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a wasu jaridun kasar guda biyu.
Kotun, a wani hukunci da mai shari’a Anwuli Chikere ya yanke, ta ce korar Sanusi daga kan karagar mulki sarautar Kano ya sabawa ka’ida, kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, kuma ya yi matukar tauye hakkinsa na dan Adam.
Don haka, ta Umarci Gwamnatin Kanon ta baiwa Sanusin diyyar Naira miliyan 10,
Yayin da yake gabatar da takaitaccen bayani na karshe, lauyan Sanusi, Abubakar Mahmoud, SAN, ya shaida wa kotun cewa wanda yake karewa ba kalubalantar tsige shi.
Mahmoud ya ce wanda yake karewa ya Kawo kara gaban kotu kan yadda ake tauye masa hakki dangane da aka yi masa bayan da gwamnatin jihar Kano ta tsige shi