Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Gwamnatin jihar Kano ta bankado wata badakala da ake yi a tsarin biyan albashin ma’aikatan kananan hukumomi,inda aka gano ma’aikata kimanin 247 da watakila ko sun yi ritaya daga aiki ko kuma sun mutu, amma ana cigaba da cire kudaden albashinsu.
Kadaura24 ta rawaito cewa bincike ne ya nuna cewa sunayen ma’aikatan kananan hukumomin da abin ya shafa ya bayyana a cikin jerin sunayen ma’aikatan da ake biyansu albashi.

Wata sanarwa da sakataren yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar Musa Tanko Muhammad ya fitar, ta ce kudaden da ake biyan wadancan mutane a watan maris din 2025 kadai sun kai naira biliyan 27,824,395.40 .
“A wani gagarumin yunkuri na tsaftace albashin ma’aikatan jihar, gwamnatin jihar Kano ta samu gagarumar nasara a kokarinta na sake fasalin tsarin biyan albashin ma’aikatan jihar.
Hajjin bana: Saudiyya ta fitar da jerin Harsuna 20 da za a fassara hudubar Arfat da su
Tun daga aikin tantancewa ma’aikatan da aka yi, aka gano wata matsala mai tayar da hankali a cikin tsarin biyan albashin na kananan hukumomi.
“A kokarin gwamnatin jihar Kano na magance wannan matsala, an gano kudaden da kuma wadanda su ke aikata laifin, sannan za a mayar da kudaden a Asusun ajiya na kananan hukumomi”. A cewar sanarwar
“Gwamnati ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta inganta tare da kawar da duk wata tsari na almundahana a tsarin biyan albashin ma’aikatan jihar Kano.
Sanarwar ta kara da cewa, za a gano mutanen da suke da hannu a wannan almundahanar tare da gurfanar da su don a ladabtar da su.