Yadda za mu koyawa Matasa 5000 Noman zamani – Shugaban hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Shugaban hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are Engr Rabi’u Sulaiman Bichi ya yi alkawarin koyawa matasa akalla dubu biyar dabarun noma na zamani da domin samar musu da aikin yi da kuma wadata kasar nan da abinchi.

” A shekarar mu ta farko a ofis mu na da burin koyawa matasa 5000 noman rani na zamani don su dogara da kawunansu da kuma wadata Nigeria da abinchi kamar yadda shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yake fata”.

FB IMG 1744283415267
Talla

Engr. Rabi’u Sulaiman Bichi ya bayyana hakan ne a wani bangare na jawabin da ya gabatar lokacin da ya karbi ragamar jagorantar hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are.

Musa Iliyasu Kwankwaso, Rabi’u Sulaiman Bichi sun kama aikin da Tinubu ya ba su

Ya ce Idan an koyawa matasan noman zamani hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are zata hada su da bankin ba da lamuni kan harkokin noma domin ya ba su jari, sannan a hada su da hukumomin da suka dace domin tallafa musu wajen samar musu da masana’antu da kasuwannin da za su rika sayar da kayan da za su rika nomas.

Rabi’u Sulaiman Bichi ya ce matasa su ne kashin bayan cigaban ko wacce al’umma, don haka duk kasar da ta ke son cimma manufofinta da samun cigaba dole ta sanya matasa a gaba wajen koya musu sana’o’in dogaro da kai.

InShot 20250309 102403344

Ya ce hukumar za ta fito da sabbin tsare-tsaren yadda za ta inganta harkokin noma da kuma samar da kayan aikin noma na zamani domin kaucewa tsohon tsarin noman da ake amfani da karfi a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...