Daga Rahama Umar Kwaru
A ranar Juma’a Nan 11 ga watan Afrilu tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a gidansa dake Kaduna.
A cikin wani faifan bidiyo da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023 Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce ya kai wa Buhari ziyarar bayan Sallah.

Bidiyon da Kadaura24 ta gani a yan tawagar Atikun akwai tsofaffin gwamnonin jihohin Sokoto da Kaduna, Aminu Tambuwal da Nasir El-Rufai.
A cikin sakon nasa, Atiku ya ce tsohon shugaban kasar kamar yadda ya saba ya rika yi musu barkwanci a lokacin da suka hadu da shi yau a gidansa.
Damina: Gwamnati ta bayyana jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar ruwa a Nigeria
Ya rubuta cewa, “A matsayina na Wazirin Adamawa, na kasance a Adamawa lokacin bukukuwan Sallah, inda na kasance tare da Lamido Fombina (Adamawa) a wasu taruka na bukukuwan Sallah.
“A yau, na samu damar kai wa Mai Girma Muhammadu Buhari, tsohon Shugaban Tarayyar Najeriya ziyara bayan Sallah, 2015-2023.