An Samar da Sabuwar Manhajar Kallon Fina-finan Hausa Mai Suna Kallo

Date:

 

Mu na farin cikin sanar da ku manhajar nishaɗantarwa ta yanar gizo mai suna kallo.

An ƙirƙiri manhajar kallo.ng ne domin sada masoya nishaɗi, musamman ma masoya fina-finan Hausa daga wayoyinsu na hannu ko kwamfutarsu a gida ko a wajen sana’o’insu Cikin Sauki ba tare da wata matsala ba.

Manhajar Kallo.ng za ta kawo muku daɗaɗan shirye-shirye da sabbin fina-finai, fina-finai masu dogon zango, shirye-shirye na musamman da kuma kaɗe-kaɗe iri daban-daban.

Za ku iya shan kallo shirye-shiryen  a adreshin su na yanar gizo, ko ku sauke manhajar kallo a na’ura mai ƙwaƙwalwa, wayoyin andiroyid ko kuma iOS wanda zai zo muku nan ba da daɗewa ba.

Burin su shi ne su nishaɗantar da ƴan nahiyar Afrika da kuma waɗan da ke zaune a ƙasashen waje ta hanyar kawo musu kayatattun shirye-shirye domin ci gaban al’adu da mu’amular mu, ta yadda za mu matso da ƴan Afrika kusa da gida ko a ina su ke a faɗin duniya ta amfani da manhajar mu da bata katsewa.

Tabbas muna sane da irin rawar da fina-finan Hausa ke takawa wajen haɗa kan al’umma ta hanyar sadar da masu kallo daga gurare daban-daban domin ilimantarwa da kuma saka ko kuma kawo canji ga masu kallo da hada kan al’umma domin kawo ci gaban al’adunmu.

Ko shakka babu Kannywood ita ce uwa-ma-bada-mama a harkar shirya fina-finan Hausa. Da haka ne za mu haɗa hannu dasu domin kawo canji mai kyau ta hanyar haɗin gwiwa da karbar changin da zamani ya kawo.

Wannan ne ya sanya kuna zaune a gidajen ku za mu riƙa kawo muku dina-finai na da waɗan da su ka yi tashe a shekarun da su ka gabata, da kuma na zamani.

Babu tantama cewa an san hausawa da son nishaɗi, to ga kallo.ng za ta share muku hawayen ku.

Kallo.ng na ƙarƙashin Spacekraft Media Limited, kamfani ne na gida wanda ya ke mallakar wasu yan kasa masu ra’ayin ci gaban al’adunsu.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...