Yan Sanda a Zamfara sun Kama Wata Mata Mai Kaiwa yan Bindiga Makamai

Date:

Jami’an tsaron ‘yan sanda da Hadin gwiwar Wasu kawarrarun Jami’an tsaro a jihar Zamfara sun kama Wata Mai Suna Fatima Lauwali bisa zargin tana safarar Makamai ga Yan Bindiga a Jihar.

Ana zarginta da bayar da makamai da alburusai ga ‘yan bindiga a jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Katsina, da Neja.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Ayuba Elkana, wanda ya yi holin wadda ake zargin a Gusau a ranar Juma’a, ya ce an kama Fatima mai shekaru 30 a unguwar Gada Biyu da ke karamar hukumar Bungudu, dauke da harsashi guda 991 na AK47 a hannunta, inda ta ce ta na jigilar su ne daga Dabagi Wani Kauye a jihar Sokoto ga wani da ake zargin Dan Bindiga ne mai suna Ado Alero.

A cewar kwamishinan, ta tabbatar da aikata laifin.

CP Elkana, da Tactical Operatives, da kuma hukumar FBI daga hedikwatar rundunar, karkashin jagorancin DSP Hussaini Gimba, sun kuma kama wani Babuga Abubakar bisa zarginsa da laifin taimakawa shugaban ‘yan bindiga, Lawali Na’eka, a karamar hukumar Maradun.

A Gusau, Babuga, Lawali, da Almeriya sun yi awon gaba da shanu 240, a cewar jagoran ‘yan sandan.

Sauran wadanda ake zargin kuma an kama ne bisa yunkurin fyade ga wata karamar yarinya, yunƙurin kisan kai, fashi, da kuma taimakawa ‘yan fashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...