An Cigaba da Sauraron Shari’ar Abduljabbar kabara

Date:

Daga Saminu Ibrahim Magashi
Kotun shari’ar musulunci Mai lamba daya dake kofar kudu karkashin jagornacin mai shari’a Ibrahim sarki Yola kotun ta zauna a Yau alhamis l damisalin karfe 9 na safiiya domin cigaba da sauraron shari’ar da ake tuhumar Abduljabbar da batanci ga ma’aiki (S A W).
A Yau katun ta dora da sauraron shedu,Inda shaidan da ya bayyana gaban kotu aka kuma baiwa Wanda ake kara wato Abduljabbar kabara damar cigaba da yiwa shaidan tambayoyi, bayan da ya kammala tambayoyin ne kotun sake bashi damar sukar tambayoyin da shaidan ya bayar da kuma wadanda ya gaza amsawa.
Abduljabbar ya kuma roki kotun da karta karbi shaidar mutumin Saboda malamin yace shaidar makiyinsa ne, kazalika suna da sabanin fahimta a addini, domin kuwa ba dalibinsabane Kamar yanda ya baiyanawa kotu tun a farko.
Abduljabbar ya Kuma bayyanawa kotun cewa Wannan shaidar ya ciwa malamin fuska yafi sau shurin masaki a kafar sada zumunta ta Facebook, bugu da kari kuma wanann sheda har littafi ya rubuta Wanda karara shedar yake ciwa abduljabbar kabaran da kuma mahaifinsa fuska. Yace dogaro da hakanne ya sa shari’ar musulunci da kanta ta hana karbar shaidar mai shedar.
A nasu bangaren  lauyoyin Gwamnati sun yi Suka kan Wannan kalami na Abduljabbar, inda su kace ba dalili bane dan kana da sabanin fahimta da wani ace shari’a ba zata karbi shaidar saba.
 Bayan kammala sauraren kowanne bangarene kotun tace zata bayyana matsayar ta kan yiwuwar amsar shaidar ko akasin haka.
Dagananne wanda ake kara ya kara rokon kotun da ta kara gabatar masa da mai bada shaida na uku domin ya yi masa tambayoyi, Sai dai lauyoyin gwamnati sun bayyanawa kotun cewa ba su zo da shaida na uku ba, Kuma Suka roki  a daga musu zuwa Zama nagaba.
 Nan take Alkalin kotun malam Ibrahim Sarki Yola ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 9/12/2021 domin Cigaba da sauraron Shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...