Matatar Dangote ta sanar da dakatar da sayar da Man Fetur da Naira na wucin gadi.
Kamfanin ya bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ya aike wa dillalan man fetur a ranar Larabar nan .
“Ya zuwa yanzu, mun sayar da sama da adadin man fetur da muka samu a Naira.

“Domin daidaita cinikayyarmu da sayen ɗanyen mai, dole ne mu ɗauki wannan mataki na wucin gadi,” in ji sanarwar.
Kamfanin Dangote ya kuma ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya dakatar da sayar da man.
Kamfanin ya ce wannan labari ba gaskiya ba ne, inda ya jaddada cewa tsarinsa yana da inganci kuma ba a samu wata matsala ba.
Gwamnan Kano ya Bayyana Matsayarsa Game da Hawan Sallah Karama a Jihar
Matatar ta Dangote ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sayar da mai a Naira da zarar ta samu ɗanyen mai da aka sayar mata a Naira daga kamfanin NNPC.
“Muna nan daram wajen yi wa kasuwar Najeriya hidima, kuma za mu dawo da sayar da mai a Naira da zarar mun samu kaya,” in ji sanarwar.