Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnatin jihar Kano ta umarci dukkan ma’aikatan jihar da su gabatar da kawunansu domin tantancesu gabanin biyansu albashin watan Maris .
Kadaura24 ta rawaito Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ibrahim Faruk ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa ranar Litinin.
Ya bayyana cewa an dauki matakin domin magance yawan korafe-korafen da ma’aikatan suka yi na samun matsalolin a albashinsu na watan Janairu da Fabrairu.

“Za a kafe Sunayen ma’aikatan da ake biya albashi a ma’aikatu da hukumomin jihar da ma sakatariyar kananan hukumomi 44 na jihar don sauƙaƙe aikin,” in ji Faruk.
Ya kara da cewa an umurci ma’aikatan da su je ma’aikatunsu don mika sunayensu tare da kai rahoton duk wata matsala da suka samu domin daukar matakin gaggawa.
Domin sa ido kan aikin tantancewar gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin shugaban ma’aikata Alhaji Abdullahi Musa. A cewar Faruk, “An bukaci kwamitin da ya gaggauta aiwatar da aikin domin baiwa gwamnati damar biyan albashin watan Maris a daidai lokacin da ya kamata.”
Yanzu-yanzu: EFCC ta bayyana dalilan da su ka sa ta kama Jarumar Tiktok Murja Kunya
Ya kuma bai wa ma’aikatan tabbacin cewa aikin tantance war ba zai kawo cikas ga ayyukan gwamnati a ma’aikatu da sakatariyoyin kananan hukumomi ba, saboda an dauki matakan da za su hana hakan.
Yayin da bikin Eid-el-Fitr ke gabatowa, Faruk ya jaddada aniyar gwamnati na ganin an biya albashi kafin sallah.
Sakataren gwamnatin Kano ya bukaci ma’aikatan gwamnatin da su baiwa wadanda za su yi aikin tantancewar hadin kai don su kammala aikin cikin nasara.