Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, tare da komawa jam’iyyar SDP.
Hakan ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yi na inda tsohon gwamnan zai nufa bayan raba gari da jam’iyyar APC.

A ranar Litinin ne El-Rufa’i ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce: “yanzu na yanke shawarar komawa jam’iyyar Social Democratic Party, kuma zan kasance a cikin ta wajen tafiyar da al’amurana na siyasa a nan gaba.
ziyarci ofishin jam’iyyar ta SDP tare da yankan katin zama ɗan jam’iyya.
2027: Atiku Abubakar ya bayyana matsayarsa game da kasancewarsa a PDP
Kwanakin baya a lokacin tattaunawarsa da kafar talabijin ta Arise, El-Rufa’i ya bayyana cewa “jam’iyyar APC ta sauka daga kan manufifin da aka ƙirƙire ta.”
Ya yi zargin cewa jam’iyyar ta gaza kiran taron shugabanninta na ƙasa tsawon shekaru, wanda ya ce hakan ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar.