Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da aikin tituna 17 a cikin ƙwaryar birnin Kano.
Ya kaddamar da fara aiyukan ne a yau Asabar a shataletalen Club Road a birnin Kano.

Ya ce aikin wani ɓangare ne na ƙudurin gwamnatin sa na gyaran birnin Kano, inda ya tabbatar da cewa aikin zai bunƙasa harkokin sufuri da kasuwanci da kuma fito da kimar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24.
Dan uwan gwamnan Kano ya bar NNPP Kwankwasiyya
Sanarwar ta ce gwamnan ya yi alkawarin za a gudanar da aiki mai inganci wanda al’ummar jihar Kano za su dade suna amfana.
Ya bukaci yan kwangilar da su tabbatar sun yi aiki mai inganci, inda ya ce musu zai rika yi musu ziyarar bazata domin ganin irin aikin da suke gudana, inda ya ba da tabbacin ba zai lamunci aiki da ha’inci ba.