Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Kwamin tsaro da yaki da fadan daba a jihar Kano ya gana da Daraktan hukumar DSS da Rundunar yan sanda da masu ruwa da sha’anin tsaro don inganta tsaro a Kano.
Shugaban kwamitin Dr. Yusuf K/Mata a ganawarsa da manema labarai ya ce sun kai ziyarar ne domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi tsaro tare da neman goyon bayan jami’an tsaro domin samun nasarar aikin da aka dorawa musu.

Sannan ya bukaci hadin kan jami’an tsaron domin magance matsalar a Jihar Kano.
Da yake karin haske kwamishinan ma’aikatar yada kabarai da al’amuran cikin gida ta Jihar Kano, Comrd. Ibrahim Waiya, ya yabawa Rundunar Yan Sanda ta Jihar Kano, bisa rawar da suke takawa wajan inganta tsaro a Jihar.
Sabon Rikici ya Barke Tsakanin Jiga Jigan NNPP Kwankwasiyya a Kano
A jawabinsa AIG Salman Dogo Garba, ya yabawa gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf bisa samar da kwamitin.
Ya kuma ce a shirye suke su bada gudunmawa wajan magance matsalar tsaro a Jihar Kano.