Assalamu alaikum wa Rahmatullah
Ina mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a Najeriya da sauran sassan duniya daban-daban su ka fara gudanar da azumin watan Ramadan.
Tabbas wannan babbar dama ce a garemu ta inganta alakarmu da Allah maɗaukakin sarki ta hanyar habaka ibadarmu da neman yafiyarsa.

Ina amfani da wannan dama wajen kira ga al’ummar musulmi dan yin koyi da dabi’un annabin rahama amincin Allah ya tabbata a gareshi wajen nuna tausayi da jinkai da karamci da kuma taimakawa marasa karfi.
Wannan wata mai alfarma dama ce ta tunawa da marasa karfi a cikinmu tun daga ‘yan uwa da makwafta har izuwa sauran al’umma.
Shekarau ya magantu kan batun sake hadewarsu da Kwankwaso
Hakazalika ina kira ga al’ummar jihar Kano da su dukufa wajen addu’o’in zaman lafiya da cigaba da yalwar arziki.
Ina yi wa kowa fatan alkairi. Allah ya karbi ibadinmu ya kuma sa mu kasance cikin bayin da zai yanta. Amin
Ramadan Kareem, Jumu’at Mubarak!