An yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya da kuma yanke mazakuta (Dandatsa) ga wasu mutum uku da aka bayyana sunayensu da John Moses, Yakubu Mohammed da Mustapha Musa, bayan kotu ta same su da laifin fyade a Kaduna.
LEADERSHIP ta rawaito cewa kwamishiniyar Ma’aikatar Kula da Harkokin Jin Kai da Ci gaban Al’umma ta Jihar Kaduna, Hajiya Rabi Salisu, ce ta bayyana hakan a Kaduna a jiya Laraba.

A cewar Kwamishiniyar, wacce ke da jajircewa wajen yaki da fyade da duk wani nau’in cin zarafin mata a jihar, ma’aikatar ta samu nasarar gurfanar da mutum uku da aka yanke musu hukunci kan laifin fyade daga watan Yuni 2024 zuwa watan Fabrairu 2025.
An sake samu tsaiko a shari’ar neman a hana kananan hukumomin Kano kudadensu
Ta bayyana hukuncin da aka yankewa mutanen a matsayin ci gaba mai kyau, kuma hakan zai zama izina ga wasu masu aikata irin wannan mugun aiki.
“Ma’aikatar ta samu hukunci a ranar 7 ga watan Yuni 2024 a gaban Mai Shari’a Nana a shari’a mai lamba KDH/KAD/57c/2023; a shari’a tsakanin Jihar Kaduna Da John Moses, inda aka same shi da laifin fyade da zina da ‘yar cikinsa, karkashin sashe na 258 (1) na kundin dokokin Penal Code na shekarar 2017 da aka gyara, sannan aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya da yanke mazakuta.”