Abubuwan dake cikin dokar tace finafinai da majalisar Kano ta yiwa garanbawul

Date:

 

 

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da yi wa dokar da ta kafa hukumar tace fina-finai gyaran fuska.

Cikin gyare-gyaren har da tilasta wa masu wuraren da ake gudanar da bukukuwa da taruka wato event centres yin rajista.

Ayyukan hukumar na ɗaukar hankali musamman a arewacin Najeriya saboda yadda ake kai ruwa rana tsakaninta da masu shirya finafinai.

InShot 20250115 195118875
Talla

Majalisar ta amince da gyaran dokar ne wadda aka kafa tun 2001 saboda yadda ɗaukar finafinai ya sauya, abin da ya sa majalisar ta ce tilas sai ana taka wa lamarin birki a wasu abubuwan don kare addini da kuma al’adu.

“Yanzu hukumar ta kara samun iko a kan abubuwa da dama,” a cewar shugaban masu rinjaye na majalisar Lawal Husaini Dala.

An sake samu tsaiko a shari’ar neman a hana kananan hukumomin Kano kudadensu

Ya ce daga yanzu babu wanda zai shigo birnin Kano ya yi ta ɗaukar fim ba tare da samun izinin hukumar ba.

A nasa ɓangare, shugaban hukumar tace fina-finan ta jihar Kano Abba El-Mustapha, ya ja hankalin masu wallafa bidiyo a kafofin sada zumunta waɗanda ake kira da content creators da su guji duk abin da zai taɓa mutuncin addini ko na al’adar bahaushe ko kuma al’ummar jihar Kano.

Ya ce za su mara wa waɗanda ke bidiyo don nishaɗi ko samun arziki, amma ba zagin mutane ba.

20250228 181700

Bugu da ƙari, El-Mustapha ya ce ƴan social media su sani cewa hukumar tace fina-finai tana da hurumi kan dukkan wani abu da ya saɓa wa addini da al’adu, inda ya ce muddin suka samu korafi akan wani bidiyo ko wani abu da aka saka a shafukan sada zumunta, to za su ɗauki mataki.

Bayanai na cewa kawo yanzu dai majalisar dokokin jihar ta Kano ta kammala nata aikin na amincewa da gyaran dokar hukumar, abin da ya rage yanzu shi ne gwamnan Kano ya sanya hannu a kai, amma babu tabbas ko zuwa yaushe ne zai yi hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...