Daga Kamal Yakubu Ali
Kungiyar kwararrun akantoci ta kasa reshen jihar Kano ta bukaci daliban dake Shirin zana jarrabawar kammala sikandire da su hada hannu da kungiyar domin tallafa musu don Zama kwararrun akantoci.
Shugaban kungiyar Abdullahi S Shehu ne ya bayyana hakan yayin da kungiyar ta ziyarci makarantar Tangaza dake kan titin Jami’ar Bayero domin wayar da kan dalibai a game da ayyukann kungiyar da Kuma tallafa musu da kayan karatu.
Malam Abdullahi Shehu yace Samar da kwararrun akantoci daga tushe shi ne zai tallafa wajan bunkasa rayuwar al’umma da Kuma basu damar dogaro da kawunansu ba tare da jiran aiki daga gwamnati ba .
Shima Anasa jawabin Shugaban kungiyar kwararrun akantoci ta kasa reshen Kano da jigawa Dr . Abubakar Umar Faruk ya bayyana cewa dukkanin harkokin rayuwa na yau da kullum suna bukatar gudunmawar kwararrun akantoci, a don haka ya bukaci dalibai dasu hada hannu da kungiyar domin ganin sun cimma burinsu na rayuwa .
Kungiyar ta bada tallafin kayan karatu ga makaranatar.
Da yake jawabin shugaban makarantar Tangaza Dr Bien ya yabawa kungiyar kwararrun akantoci ta kasa bisa zabar makarantarsu da suka yi domin basu tallafin kayan karatu da Kuma wayar da kan dalibai game da ayyukann kungiyar.
Wakilin Kadaura24 ya bamu labarin cewa taron ya samu halarta Al’ummar da dama, inda daga bisani kungiyar ta Kai ziyat makaranatar Al-Amin dake unguwar Tal’udu domin mika tallafi da wayar dakan dalibai.