Rikicin APC :Muna kokarin Sasantawa tsakanin mu da su Mal Shekarau – Sanata Kabiru Gaya

Date:

Daga Usman Aliyu

Sanatan Kano ta kudu Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya bayyana cewa Suna iya bakin kokarin su domin Sasantawa tsakanin Masu goyon bayan jam’iyyar APCn Kano da Kuma bangaren su Sanata Malam Ibrahim Shekarau .

Kadaura24 ta rawaito Sanata Kabiru Gaya ya bayyana hakan ne yayin taron Manema labarai da Yan Majalisu 20 da shi Sanatan suka Shirya don mayar da martani ga korafin da su Sanata Malam Ibrahim Shekarau suka mikawa uwar jam’iyyar ta Kasa.

Sanata Kabiru Gaya yace sun rubuta wasikar martani ga uwar jam’iyyar ta Kasa mai dauke da sa hannu yan Majalisar wakilai 20 da Kuma Sanata guda 1, Inda a ciki wasikar Suka ce babu wani rikici a jam’iyyar APC a Kano Kamar yadda daya bangaren suka ambata a wasikarsu.

Yace duk wani Mataki da Gwamna Ganduje zai dauka a jam’iyyar APC ta jihar Kano sai ya tuntubi duk masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, yace Ganduje bai taba daukar Wani Mataki ba tare da sanin mu ba.

“Karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje an gudanar da zaben Shugabanin jam’iyyar a matakan mazabu 484 da Kananan Hukumomi 44 lami lafiya ba tare da Wata matsala ba, don haka ba dai-dai bane ace wai ba’a yi sahihin Zabe ba a Kano.” Inji Kabiru Gaya

“Wadancan Masu korafin Yan uwanmu ne don haka muke Kira a garesu da su Zo mu hada hannu waje guda domin Samun Nasara Jam’iyyarmu ta APC a Zabe Mai zuwa”. Sanata Gaya

Sanata Gaya ya bayyana cewa suna Sanar da uwar jam’iyyar ta Kasa karkashin jagorancin Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni Cewa babu wani rikici a jam’iyyar Kuma Suna tare da jagorancinsa da Shugaban Kasa Muhd Buhari da Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje don haka suke Kira da Shugabanci da yayi watsi da waccen takardar koke da Wasu tsiraru cikinsu Suka rubuta.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...