Daga Ibrahim Sani Mai Nasara
An sanar da rasuwar Sarkin Tsaftar Kano Alhaji Jafar Ahmed Gwarzo a yau Laraba.
Alhaji Jafar ya rasu ne a yau bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a kasar Saudiyya.
Kafin rasuwarsa, Sarkin ya kasance babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje kan rigakafin cutar shan inna.
Da yake tabbatar da rasuwar sa ga manema labarai, wani makusanci marigayin Alhaji Nasiru Sani Gwarzo ya ce, marigayi Jafar Gwarzo ya tafi kasar Saudiyya domin yin Umrah kwanakin baya.
Marigayin ya rasu ya bar mata da ’ya’ya da dama.