Sabbin Matakan tsaro da ya kamata al’ummar Kano su bi a watan Ramadana – Inji Rundunar Yansanda

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar Kano ta fita da wasu sabbin matakan tsaro a watan azumin Ramadan, a kokarinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kadaura24 ta rawaito Rundunar ta ce ta yi isassun tsare-tsare na tsaro domin tabbatar da an gudanar da azumin watan Ramadan cikin lumana da nasara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar yansanda ta Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ga shawarwarin da rundunar ta baiwa al’ummar Kano.

– Masu zuwa Allah asham su kauracewa daukar abubuwan da ba zama dole ba, amma ba laifi su tafi da dadduma (Sallaya) don rage zato.

– Ya kamata mutanen da ke halartar Masallatan da ake gudanar da Tafsiri su yi taka-tsan-tsan, tare da kai rahoton duk wani abu ko motsin da ba su aminta da shi ba ga jami’an tsaro.

Yanzu-Yanzu: An ga Watan Ramadan a Ƙasar Saudiyya

– Dole ne masu ababen hawa su bi ka’idojin tuki, da guje wa tukin ganganci, don kaucewa hatsari.

– An haramta wa yara ƙanana da marasa lasisi tuka da ababen hawa, da suka hadar da motocin babura da adaidaita sahu.

– A kwai bukatar Iyaye su rika raka ’ya’yansu ko hada su da manya a duk inda za su shiga a lokacin azumi don gudun bacewar yaran da hadurra.

– An kuma haramta Hawan doki ba bisa ka’ida ba, an hana yin taruka wadanda ba a nemi izini ba.

– An haramta amfani da wasa da wuta ko buga wani abu mai kara a lokacin watan na Radaman.

Rundunar Yansandan Kano ta yi Karin Haske Kan Yunkurin Kone Gidan Sarki na Nasarawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi gargadin cewa ba za a amince da duk wani nau’in daba a cikin wata mai alfarma ba. Kuma duk wani mutum ko kungiyar da aka samu tana irin wadannan ayyuka za a dauki Matakan ladabtarwa akan su bisa doka.

Rundunar ta shawarci jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaron da suka hada da hukumar kiyaye hadurra ta tarayya, jami’an tsaron farin kaya, KAROTA, Hisbah, kungiyar ‘yan Vigillante, da sauran jami’an tsaron sa kai m

Rundunar ta bukaci al’ummar Kano da su kai rahoton duk wani abu da basu yarda da shi ba ta hanyar kiran wadannan lambobin 08032419754, 08123821575, 09029292926.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba za mu lamunci cin zarafi ko tozarta wasu da sunan Tashe ba – Hukumar Hisbah

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Hukumar Hisba ya jihar kano ta...

Da dumi-dumi: El-Rufa’i ya fice daga jam’iyyar APC

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya tabbatar da...

2027: Atiku Abubakar ya bayyana matsayarsa game da kasancewarsa a PDP

  Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin...

Cikakken Bayani Kan Yan Bindigar da Yansanda Su Ka Kama a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar...