Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Ma’aikatan gwamnatin jihar Kano sun koka da yadda gwamnatin ta ranke masu wasu kudade daga cikin kudaden albashin da aka biya su a wannan wata na fabarairu.
Kadaura24 ma’aikatan sun bayyana cewa har yanzu ba a sanar da su dalilan da suka sanya aka yankar musu albashin ba.
Wani ma’aikaci da ya nemi mu sakaye sunansa ya ce shi an yankar masa kimanin Naira 2500 daga cikin albashin sa , yayin da ya ce akwai wanda cikin abokan aikinsa aka yankar masa kimanin Naira 8000 wani kuma Naira 9000.
” Abun ya ba mu mamaki yadda aka yanke mana kudi ba tare da an sanar da mu dalilin yin hakan ba, kuma ba mu ma san wa za mu tunkara don sanin matsalar ba”.Inji Shi

” Abun ta kaicin ma shi ne an yankar mana kudin a daidai lokacin da muke bukatar kari akan albashin na mu, saboda siyayyar azumin watan Ramadana, ga batun kayan sallar yara”.
Ita ma wata ma’akaci ta nuna damuwa da abun da aka yankar musu ba tare da sanin dalili ba, amma dai wasu suna tunanin kudin da aka yankar musu yana da nasaba da sake mayar da ma’aikatan Kano cikin shirin Bankin ba da lamunin gidaje na gwamnatin tarayya, amma dai hakan ba tabbas.
Gwamnatin Kano ta horar da jami’an yada labaran jihar dabarun sadarwar na zamani
Da yake jawabin ga manema labarai kan makasudin yankar kudaden albashin na su na wannan wata, sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Umar Faruq Ibrahim ya ce gwamnan Kano bai san dalilin da yasa aka yiwa ma’aikatan haka ba .
“Wannan labari bai yiwa gwamnan Kano dadi ba, hakan ta sa ya kafa kwamiti domin ya binciko dalilin yankarwa ma’aikatan kudin ba”. Inji Umar Faruq Ibrahim
Ya ce an kafa kwamitin ne karkashin kwamishinan raya karkara na jihar Kano Alhaji Abdulkarim Abdulsalam domin gudanar da bincike cikin gaggawa don magance matsalar .
Sakataren Gwamnatin ya ce wadanda aka sanya a kwamitin dukkaninsu kwararru ne kan sha’anin kudi da fasahar zamani, inda ya ce an yi hakan ne domin ganin an binciko matsalar cikin gaggawa don magance ta.