Daga Rahama Umar Kwaru
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’adu Abubakar III ya bukaci al’ummar Musulmi dake fadin Nigeria da su fita fara duban jinjirin watan Ramadana a gobe JUMA’A 29 ga Watan SHA’ABAN, 1446AH daidai da 28/2/22025.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin harkokin addinin musulunci na fadar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo wali Junaidu ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ce gobe Juma’a ita ce 29 ga watan sha’aban kuma ita rana ta farko da ya kamata al’ummar Musulmi su fara duba jinjirin watan Ramadana na Wannan Shekarar.
Fargaba: An tsaurara tsaro a Gidan Sarki na Nasarawa inda Aminu Ado Bayero ke zaune
Sanarwar ta ce Idan Allah yasa anga watan sai a sanar da wani basarake mafi kusa domin isar da sakon ga Sarkin Musulmi ko a kira wadannan numbobin domin isar da sakon kai tsaye ga majalisar Sarkin Musulmi.
1.08037157100
2. 08066303077
3. 08035965322
4. 08099945903
5. 07067146900