Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Majalisar limaman masallatan Juma’a ta kasa karkashin jagorancin shugabanta Sheikh Muhammad Nasiru Adam, ta bayyana goyon bayanta ga shirin gwamnatin jihar Kano na tantance kungiyoyi masu zaman kansu.
Sheikh Muhammad Nasiru Adam ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Litinin.
Sheikh Muhammad Nasiru Adam shi ne babban limamin masallacin Sheikh Ahmad Tijjani dake kofar mata a tsakiyar birnin Kano.
Sheikh Muhammad Nasiru Adam ya ce “Muna goyon bayan gwamnatin jihar Kano a kan matakin da ta dauka na tantance kungiyoyi masu zaman kansu.”

Sheikh Muhammad Nasiru Adam ya jaddada mahimmancin tantance kungiyoyi masu zaman kansu, inda ya bayyana cewa wasu ayyukan kungiyoyin sun sabawa al’ada, da addinin mutanen Kano.
Zargin batanci: Kotu ta aikewa Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki sammaci
Ya bayyana cewa wadannan ayyuka a wasu lokuta suna yin illa ga zamantakewar al’ummar Kano.
Sheikh Muhammad Nasiru Adam ya kara da cewa Majalisar Limaman Juma’a ta himmatu wajen aiwatar da ayyukan da suke taimakawa da kuma amfanar addinin Musulunci.