Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Date:

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin shugabannin hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa ta jihar Kano domin tabbatar da adalci da kare hakkin masu sayen kaya a dukkanin kasuwannin jihar Kano.

Hakan na kunshe cikin wata samarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24.

InShot 20250115 195118875
Talla

Kunshin wakilan hukumar sun hada masana da kwararru da jami’an gwamnati da kuma wakilcin yan kasuwa domin tabbatar da daidaito da adalci a gudanarwar hukumar.

Sanarwar ta bayyana Dr. Umar Garba Haruna a matsayin shugaba yayin da Alhaji Zangina Jafaru zai kasance a matsayin babban sakataren hukumar.

Aiyuka 5 da Gwamnan Kano ya yi alkawarin yi, bayan dakatar da rusau a Rimin Zakara

Sauran wakilan hukumar sun hada da Alhaji Ibrahim Ahmad Gama daga Kano ta tsakiya da Hajiya Safiya Umar Bichi daga Kano ta Arewa da Alhaji Hussaini Bello Gidado daga Kano ta Kudu.

Kazalika kunshin wakilan hukumar ya hada da Alhaji Munzali Abubakar daga Kasuwar Kantin kwari da Alhaji Muhammad Adakawa daga kwanar singa da Alhaji Ahmad Isa Chedi daga Kasuwar Dawanau da Alhaji Sani Gambon daga Sabon gari.

Sauran wakilan hukumar sun kunshi jami’ai daga ma’aikatar Sharia da ta lafiya da ta Mahalli da kuma ma’aikatar sufuri.

Sanarwar ta bukaci sabbin wakilan hukumar da su fara aiki nan take domin kawo karshen korafe-korafe tsakanin mai saye da mai sayarwa da kuma tsaftace al’amuran Kasuwanci a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba wani maniyaci dan Nigeria da zai rasa Aikin Hajjin bana – Shugaban NAHCON

Daga Isa Ahmad Getso   Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON),...

Atiku Abubakar ya yi ganawar sirri da Obasanjo

Dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyar PDP a zaɓen...

Ku mai da hankali wajen gina rayuwar al’umma – Sarkin Kano na 16 ga Kungiyar matan Arewa

Daga Sani Idris maiwaya   Sarkin Kano na 16 Khalifa Muhammad...

Rundunar yansandan Kano ta baiwa al’ummar Sheka kwana 1 su kai mata Sunayen yan daban unguwar

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin...