Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Wata gobara da ta tashi ta yi sanadin mutuwar almajirai 17, sannan 15 kuma suka sami saunuka a karamar hukumar kauran Namoda dake jihar Zamfara.
Wutar dai ta tashi ne da misalin 20:00 na daren jiya, inda wutar ta tashi lokacin da suke barci sanadiyya wasu karare da ake ajiye wa a gidan da almajirai suke kwana.
Malam Aliyu Abubakar Khalifa wanda shi ne malamin almajiran ya shaidawa majiyar Kadaura24 cewa almajirai yan kimani shekaru 10 zuwa 16 ne lamarin ya rutsa da su.
Malami Khalifa ya tabbatar da cewa cikin yara sama da 100 da suke kwana a gidan,17 ne suka rasu yayin da kuma 15 suka sami raunuka.
Mutanen gari sun yi iya kokarinsu don ganin an kashe wutar amma abun yaci tura.
An sanar da hukumar kashe gobara ta jihar dake da ofishi a kauran Namoda, amma masu sami damar zuwa su kawo dauki ba saboda motar kashe gobara ta Kaura Namoda ba tada Lafiyar da zata iya kai daukin.
Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano
Hukumar kashe gobara ta jihar ta bakin PFS Abdulwahab Muhammad Galadi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun kasa zuwa wurin da lamarin ya faru ne saboda wasu matsaloli da suke fuskanta.
Haka ita ma Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta bakin mai magana da yawunta DSP Yazid Abubakar ya tabbatar da cewa yara 17 sun rasu yayin faruwar lamarin .
Inda ya ce wadanda kuma suka jikkata suna asibiti suna karbar magunguna.
Wasu daga cikin al’ummar garin dai sun dora alhakin rasuwar almajiran akan gwamnatin jihar, saboda da yan kwana-kwanan sun kai dauki watakila da barnar da wutar ta yi ba ta kai haka ba.
Rahotannin da jaridar Kadaura24 ta samu sun nuna cewa an kai wadanda suka samu raunuka asibiti, amma bandaji kawai aka saka musu sannan aka dawo da su gida.