Daga Nazifi Dukawa
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano yadda wasu mutane yan jihar Bauchi suke shigowa dazukan jihar domin yin aiki gona ba tare da izini ba.
Mai baiwa gwamna shawara kan tsirrai da manun daji da gandun daji Hon Halliru Ahmad Sawaba ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da Kadaura24, Jim kadan bayan wata ziyara da suka kai dajin falgore dake karamar hukumar Doguwa.
Ya ce gwamnatin jihar Kano ba zata lamunci irin wannan dabi’ar ba , inda ya ce za su dauki matakan da suka dace domin dakatar da faruwar hakan a nan gaba.
“Yau kwanan mu biyar a Wannan Daji na na Falgore mun kuma kewaya domin tabbatar da dokar ta bacin da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanya ta hana sare bishoyoyi”.
Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5
” Gwamnan Kano ya dauki Wannan matakin ne domin inganta muhalli da kuma tabbatar da cewa dazukan mu sun cigaba da kasance a yadda suke saboda amfanin da suke da shi ga al’umma”. Inji Hon Halliru Ahmad Sawaba
Ya ce za su sanar da gwamnan Kano cewa akwai bukatar a karowa ma’aikatan dake kula da Dajin na Falgore kayan aiki wadanda suka hadar da motoci da babura domin yin sintiri don tabbatar ba a karya dokar da gwamnan ya sanya.
Ya kuma yabawa ma’aikatan bisa jajircewar da suke wajen gudanar da aikinsu, sannan ya ba da tabbacin gwamnatin jihar Kano ba zata saurarawa duk wanda aka kama yana sare bishoyoyi a dazukan jihar Kano ba .
Da yake nasa jawabin shugaban dake kula da Dajin na Falgore Isham Sani Aliyu ya yabawa mai taimakawa gwamnan bisa ziyarar da ya kai da kuma yadda ya nuna damuwa Kan matsalolin da su ma’aikatan suke fuskanta wajen gudanar da aikinsu.
Ya bayyana cewa daga cikin matsalolin da suke fuskanta akwai karanci ma’aikata da karanci motoci da mashina domin yin sintiri don tabbatar da ba a yin wata barna a dajin, domin ya ce muddin aka bari aka cigaba da sare bishoyoyin dake dajin na falgore to akwai barazanar gafewar madatsun ruwa na jihar musamman ma madatsar ruwa ta Tiga.