Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta biya diyya ga wadanda aka kashe ya’yansu a yayin rushe wasu gine-gine a Rimin Zakara da ke jihar.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a ranar Lahadin da ta gabata ne tawagar jami’an tsaro ta hadin gwiwa suka bude wuta, inda suka kashe mutane hudu tare da raunata wasu da dama a yayin rushe wasu gine-ginen da aka gina ba bisa ka’ida ba a wasu filaye na jami’ar Bayero ta Kano (BUK) .
Gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Wayya, ya mayar da martani game da kashe-kashen, inda ya ce za a kafa kwamitin da zai binciki lamarin.
Kwankwaso ya ce: “ Ya kamata gwamna Abba Kabir Yusuf da kansa tare da kwamishinonin sa na kasa da ayyuka su kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a rikicin.
Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya
“Har ila yau, ya kamata gwamnati ta gaggauta fara biyan diyyar gidaje da gine-ginen da aka rushe tare da biyan diyyar rayukan da aka rasa.
“Na yarda da abun da Amnesty International ta ce na kiran da ta yiwa gwamnatin jihar Kano ta dakatar da kai hare-hare kan al’ummomin da ke fama da talauci wadanda ake azabtarwa shekara da shekaru”. Inji Kwankwaso
Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce yana amfani da damar wajen kara mika sakonsa na ta’aziyya ga wandanda aka kashewa ya’yansu da kuma jajantawa mutanen da aka raunata.