Daga Sani Idris maiwaya
Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj Ibrahim Imam ya ce za su duba yiyuwar Kara Alwawus din da su ke baiwa Limamai da Ladanai na Karamar hukumar Dala.
Alhaji Suraj Imam ya bayyana hakan ne yayin wani taro da limaman masallatai dake yankin karamar hukumar Dala .
yana Mai cewar tabbas limaman da Ladanai suna da matukar mahinmanci a tsakakanin al’umma.
Cikin wata sanarwa da Jami’ar Yada labaran karamar hukumar Dala Hassana Aminu ta aikowa Kadaura24, ta ce
Surajo Imam yace ya zama wajibi su sake yin duba akan alawus din da ke basu duk wata su da ladanai da na’ibansu, inda yace za a yi duba da yanayin da ake ciki rayuwa .
Haka Kuma Shugaban karamar hukumar ya karbi kukansu na gabatar da bita akan yadda zasu fahimci abin da ake nufi da gwaji kafin aure idan an gabatar musu da sakamakon .tare da yin kira a gare su akan yiwa shugabanni addu’ar Allah ya taimake su wajen cigaba da gudanar da managartar ayyukun raya kasa .
Rusau: Ana zargin an harbi mutane 6 a unguwar Rimin zakara dake Kano
Da yake nasa jawabin shugaban limaman masallatai na yankin dala malam Nura Arzai kuma limamin masallacin Ah’hababu na mariya sunusi Dantata dake Kofar Ruwa ya bayyana jin dadinsa bisa wannan gayyatar , inda yace dama jira suke a kira su , sannan zasu cigaba da kokari akan tarbiyantar da yara masu tasowa .
Malam Nura Arzai yace karamar hukumar Dala tana da masallatai guda 34 da limamai da ladanai da na’ibai wanda aka yi su na’ibai na daya da na biyu .
Malam nura arzai yayi kira ga gwamnati data mai da hankali akan gina makarantun kur’ani da islamiyya, inda yace Idan akai hakan tattalin arzikin kasar zai gyaru.
A jawabansu daban-daban imam Bukar Abubakar da imam Isah Abba umar Madabo sun yi kira ga shugaban karamar hukumar Dalan da yaji tsoron Allah yayi mulki bisa gaskiya da amana ya tsaya akan tafarkin da yayi alkhawari .