Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Date:

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa

 

Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills karkashin jagorancin Shugaban kamfanin Alh. Ibrahim Muhammad Gerawa, ya ba da gudunmawar na’ura mai kwakwalwa (Computers) guda dari domin amfanin daliban yankin da kamfanin yake dama al’ummar garin Gezawa baki daya.

” Mun kawo wadannan na’urori masu kwakwalwar ne a wani bangare na hidimtawa al’ummar da muke aiki a yankinsu, don inganta rayuwar daliban yankin dama makwaftansu”.

A yayin taron mika Kwamfutocin wanda Alhaji Muhammad Isyaku wanda shi ne Shugaban rukunin kamfanin Gerawan ya jagoranta, ya ce sun bada wannan gudunmawar ne domin kara inganta ilimin na’ura mai kwakwalwa musamman ga dalibai masu hazaka da basira a yankin.

InShot 20250115 195118875
Talla

” Muna taimakawa mutane da suke aiki a cikinsu, amma Wannan shi ne karon farko da muka kawo irin wannan tallafin gare ku a fanni ilimi, kuma muna ba ku tabbacin zan kamfanin Gerawa zai cigaba da tallafawa muku a fanni ilimi da sauran fannonin rayuwa”. Inji Alhaji Muhammad Isyaku

Alhaji Muhammad Isyaku ya bukaci al’ummar garin Gezawa da su Alkinta wadanan na’ura mai kwakwalwa domin su ci gajiyar su baki daya .

Da yake godewa Shugaban kamfanin Gerawa a madadin al’ummar garin Gezawa Barr. Muhd Sani Yunusa Shugaban kungiyar gezawa Collation bayan ya godewa Shugaban kamfanin na Gerawa Alhaji Ibrahim Gerawa ya ba da tabbacin za su yi duk mai yiwuwa don ganin sun alkinta kayan.

Rusau: Ana zargin an harbi mutane 6 a unguwar Rimin zakara dake Kano

“Babu shakka wadannan na’urori masu kwakwalwa za su taimaka matuka wajen inganta ilimi da rayuwar matasa da al’umma karamar hukumar Gezawa, kuma Ina kira ga saukaran kamfanoni da su yi koyi da abun da kamfanin Gerawa yayi”. Inji Shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Mamallakin jaridar Nigerian Tracker ya zama Ma’ajin kungiyar masu yada labarai a kafar yanar gizo ta Arewa

Kungiyar masu yada labarai a kafafen sadarwa na zamani...