Shugaban gidan Rediyon jihar Kano Kwamared Abubakar Adamu Rano ya ce yasawa ransa cewa tafiyar Kwankwasiyya da yake yi tamkar ibada ce.
” Na gamsu da yadda Kwankwasiyya take taimakon al’umma, kuma har a wajen Allah zan iya kare kaina game da dalilin da yasa na shiga Kwankwasiyya har na gamsu da tsarin tafiyar”.
Kadaura24 ta rawaito Abubakar Adamu Rano ya bayyana hakan yayin wata hira da yayi da Express Radio dake Kano cikin shirin barka da Safiya na ranar talata.

” Akwai dan uwan jagora Rabi’u Musa Kwankwaso da na sani wanda aka ki biya masa kudin ka karo karatu Saboda bai chanchanta, sannan kuma nasan wanda aka biyawa kudi masu tarin yawa ya je ya karo karatu kawai don ya chanchanta ba tare da yasan wani ba, don haka na gamsu Kwankwasiyya don taimakon ya’yan talakawa aka kafa ta”. Inji Abubakar Rano
Shugaban Gidan rediyon Kano ya ce sune umarawan Kwankwasiyya wandanda suka shigo ta daga baya kuma suka yi mata rikon mutu ka raba.
Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-naden Mukamai
Da yake tsokaci dangane da batun shari’ar gwamnan Kano da aka yi a Kotun koli, Rano ya ce an so a cuci kundin tsarin mulkin Nigeria amma Allah ya kare.
“Da kotu Koli bata bayyana nasarar Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ba, da ina jiyewa Najeriya sai an sake daftarin kundun tsarin mulkin ta na ƙasa, saboda kura kuran da’aka tafka a cikin shari’ar.” A cewar, Comr. Abubakar Adamu Rano, Shugaban Gidan Radio Jihar Kano.