Wata babbar kotun Kano, a karkashin Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ta bayar da umarnin wucin gadi na hana Sufeto Janar na ‘yan sanda da hukumar ‘yan sanda gayyata ko kamawa ko kuma musgunawa Shugaban Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin-Gado.
Wadanda su ka shigar da karar sun hada da antoni janar na jihar Kano, hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da Muhuyi Magaji Rimingado.

Haka kuma wadanda ake ƙarar sun hada da rundunar ƴansandan Najeriya, Sufeto Janar na ƴansanda, AIG shiyya ta daya, kwamishinan ƴansanda na Kano, ASP Ahmed Bello da Bala Muhammad Inuwa.
An ba da umarnin ne a yau Litinin.
Gwamnatin Kano Za Ta Fara Shirin Yiwa Ali Madakin Gini Kiranye
A tuna cewa a makon da ya gabata ne rahotanni su ka baiyana cewa ƴansanda su ka kama Muhuyi tare da tsare shi tsawon awanni, inda daga bisani aka bada belin sa.
Rahotanni sun baiyana cewa an kama Muhuyi ne bisa zargin ƙwace wata kadara da ke da alaƙa da tsohon gwamnan Kano, kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.