Gwamnatin jihar Kano tayi kira ga Shugaban Kasa Bola Tinubu daya bayar da umarnin janye jami’an yan’ sanda da aka jibge a filin wasa na Sani Abacha.
Kwamishinan yada labarai Kwamaret Ibrahim Waiyya ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.
Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana cewar za’a gudanar da taron Mauludi kamar yadda aka saba gudanarwa a duk shekara.

Kwamishinan ya kara da cewar babu wani dalili da za ‘a hana mabiya darikar Tijjaniyya gudanar da taron su a gobe kamar yadda aka shirya.
Da dumi-dumi: Yan sanda sun kama Muhuyi Magaji Rimin gadon
Yakara da cewar idan akwai batun rade-raden matsalar tsaro kama yayi Gwamnatin Tarayya ta tun-tunbi gwamnatin Kano, ba kawai a kawo yan’ sanda ba.
Idan za a iya tunawa a wannan rana ta Juma’a rundunar yan sandan Kano ta fitar da sanarwa inda ta ce akwai barazanar tsaro a jihar da kuma wani kulli da suka gano na kai hari jihar.