Maulidin Inyass: Sarkin Kano na 15 ya dauki nauyin karatun Matasa 30 a Jihar Bauchi

Date:

 

Mai martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi alkawarin daukar na nauyin karatu mutane 30 a wata Makarantar kimiyya dake jihar Bauchi.

” Cikin ikon Allah, zamu dauki nauyin matasa guda 30 tun daga sayen form din Makarantar har su kammala, don inganta rayuwarsu”.

InShot 20250115 195118875
Talla

Kadaura24 ta rawaito Sarki Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron Moulidin Shehu Ibrahim Inyass wanda aka gudanar a garin Bauchi.

Ya ce yabawa mabiya darikar Tijjaniyya na Nigeria bisa yadda suka halarci taron cikin kyakykyawan yanayi, da kuma yadda suke yiwa Kasa add’o’in samun zaman lafiya a kasar.

Da dumi-dumi: Yan sanda sun kama Muhuyi Magaji Rimin gadon

” Muna godiya yadda mabiya darikar Tijjaniyya suke yi mana addu’a, musamman maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi da sauran Malamai da shehunan Darikar Tijjaniyya na duniya”.

Gabanin gudanar da taron Sarki Aminu Ado Bayero ya ziyarci fadar mai martaba Sarkin Bauchi domin sada zumunci , daga bisani a jiya da yamma kuma ya halarci taron zikirin Juma’a na kasa da aka gudanar a masallacin Juma’a na Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Dubun dubatar mabiya darikar Tijjaniyya ne daga sassa daban-daban na Nigeria da wajen kasar ne suka halarci taron, wanda aka gudanar da shi karkashin a khalifan sheik Ibrahim Inyass wato Sheikh Mahy Inyass.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...